15 Janairu 2022 - 19:32
Iran: Mutanen 18 Ne Suka Rasa Rayukansu Sanadiyar Cutar Covit 19 A Yau

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Iran ta bada sanarwan cewa mutane 18 ne suka rasa rayukansu a duk fadin kasar sanadiyar kamuwa da cutar Covid 19 a duk fadin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Majiyar ma'aikatar ta kara da cewa yawan wadanda suke rasa rayukansu saboda cutar na kara raguwa, kuma akwai fatan nan gaba kadan ba wanda zai rasa ransa sanadiyyar cutar a kasar.

Kididdiga na ma'aikatar ya nuna cewa ya zuwa yanzu an yiwa mutane 60,982,939 aka yi wa zagaye na farko na alluran riga kafin cutar a duk fadin kasar, sannan 56,640,275 suka yi zagaye na biyu sai kuma 12,205,821 ne suka yi zagaye na uku na alluran a duk fadin kasar.

Banda haka 1,421 aka tabbatar da cewa sun kamu da ita a duk fadin kasar.

342/